fbpx
Monday, May 10
Shadow

Ana caccakar Hadimin Shugaban kasa, bayan da yace ya kadu da Maganar mutuwar Auren Attajirin Duniya, Bill Gates

A jiya ne attajirin Duniya, Bill Gates ya sanar da mutuwar aurensa da matarsa,Melinda bayan Shekaru 27 suna tare.

 

Kasancewar suna tare shekaru 27 ya jawo cece-kuce sosai musamman a shafukan sada zumunta na Najeriya. Hadimin Shugaban kasa, Bashir Ahmad ba’a barshi a baya ba inda shima ya bayyana cewa ya kadu da hakan.

 

Saidai da dama sun bayyana cewa ba abinda ya kamata ya kadu dashi kenan ba, dan kuwa ga ‘yan Bindiga can zasu kashe dalibai 17 a Kaduna.

 

Wasu dai sun rika fadar cewa mutuwar aureawajan turawa ba abin tada hankali bane da jin kunya kamar yanda aka daukeshi a wasu kabilun kasashen Africa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *