fbpx
Wednesday, June 23
Shadow

Ana cece-kuce bayan ganin Ministan Shari’a, Abubakar Malami na Amfani da Twitter da Kuma Cryptocurrency duk da hana amfani dasu

Tun bayan da aka dakatar da shafin Twitter a Najeriya, Babban Lauyan Gwamnati,  Abubakar Malami ya gargadi wanda har yanzu suna amfani da shafin na Twitter.

 

Yace duk wanda aka kama za’a hukuntashi. Saidai kuma a jiya, Malami ya shiga shafin na Twitter ya goge shafinsa. Ganin cewa an haramta Amfani da shafin Twitter a Najeriya kuma Gwamnati ta yi gargadin bin barauniyar hanya ta VPN, hakan ya tabbatar da cewa, Malami shima ta barauniyar hanyar ya vi ya shiga shafin, wanda hakn ke bayyana cewa ya taka dokar gwamnati.

 

Hakanan kuma a cikin sakon da ya saki na screenshot a shafinsa na Facebook da yake sanar da cewa ya goge shafinsa na Twitter,  an ga alamar manhajar amfani da Cryptocurrency a saman wayarsa, wanda shima an haramta amfani dashi tuni.

 

Lamarin yasa ana ta cece-kuce inda da yawa suka bayyana mamaki da ganin cewa, me dokar bacci an sameshi da gyangyadi.

 

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *