fbpx
Sunday, September 26
Shadow

Ana dubu yiwuwar sake kafa dokar kullen Corona a Najeriya

Mahukunta a Najeriya sun yi gargadin cewa kasar ta fara shiga mataki na uku na annobar korona a kwanakin baya baya nan, har ma an sami kimanin mutum goma da suka kamu da sabon nau’in annobar mai suna delta.

Sai dai sun ce ana ci gaba da bin dukkan matakan da suka kamata don ganin an dakile yaduwarta.

Wani jami’i a Kwamitin Shugaban Najeriya da ke yaki da annobar korona, Dakta Muktar Muhammed, ya shaida wa BBC Hausa cewa yanzu haka mahukunta na duba yiwuwar sake kafa dokar kulle a wasu yankuna da cutar ta fi yaɗuwa.

Ya kara da cewa sai dai a wanan karon ba za ta kasance ta bai-ɗaya ba, a maimakon hakan za a yi duba da inda aka fi samun yaɗuwar cutar ne a jihohi da ma tarayya baki ɗaya.

A cewarsa, “A gaskiya a kwanakin baya mun ga cewa annobar ta ja baya, domin ba a samun masu kamuwa da cutar sosai, amma yanzu yawan ya karu, saboda mutane sun daina daukar matakan kariya, don haka ba abin mamaki ba ne idan yawan ya karu ayanzu.”

Ya ce zuwa yanzu an gano mutanen da suka kamu da cutar nau’in Delta akalla goma sha wani abu, “don haka lallai akwai wannan nau’u a Najeriya kuma yana dada karuwa, muna ma zargin cewa za a iya danganta karuwar masu kamuwa da cutar da shi wannan nau’i a yanzu haka.

Ba wani sabon abu ba ne idan kwayar cutar bairos ta hayayyafa da sauya tsarin halittarta a yayin da take yaduwa, kuma tuni masana kimiyya suka yi gargadin cewa wasu nau’ukan masu ban tsoro za su iya bijirowa.

Ko da yake har yanzu ba a kai ga sanin yadda yake yaduwa ba, amma bincike ya nuna cewa nau’in na delta yana da karin hatsari da ke tattare da yadda yake yaduwa cikin sauri.

A watan Mayu Hukumar Lafiya Ta Duniya ta ayyana nau’in na delta a matsayin “nau’in da ya kamata ya sanya damuwa”.

Ana ayyana nau’in bairos a matsayin wanda ya kamata a damu da shi sosai ne idan akwai karin shaidu da ke nuna cewa nau’in ya fi saurin yaduwa, yana kuma haifar da cutuka masu zafi sannan yana rage karfin tasirin riga-kafi da magunguna.

BBChausa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *