fbpx
Wednesday, May 12
Shadow

Ana fargabar dayawan mutane sun mutu yayin da Boko haram tayi kokarin kwace sansanin soja da ke Damasak

Sojoji, a yammacin ranar Talata, sun fafata da mayakan Boko Haram yayin da suke yunkurin karbe sansaninsu da ke Damask.
Wani mazaunin garin Damasak, a cikin karamar hukumar Mobbar na jihar Borno, a arewa maso gabashin Najeriya, ya shaidawa yan jarida cewa mutane da dama sun rasa rayukansu.
A cewar mazauna garin, ‘yan banga da suka yi kokarin dakatar da masu tayar da kayar bayan, sun ci karfinsu, inda da yawa daga cikinsu suka yi ta yawon neman sauki.
“Maharan sun kashe mutane da yawa. ‘Yan sanda ma sun gudu. Mun damu da cewa sojoji sun bar mu kuma suna kare yankinsu kawai. Amma a safiyar yau mun samu labarin cewa sojoji sun kuma fusata da jama’ar garin bisa zargin hada baki da maharan da ke ci gaba da kai hari garin Damasak.
“Maharan lokacin da suka iso jiya da misalin karfe 5:00 na yamma, kai tsaye suka nufi sansanin sojoji amma suka gamu da turjiya mai karfi. Koyaya, sojojin kawai sun fatattake su daga yankin su amma basu iya korar su daga garin ba.
“Maharan sun kwana a asibiti har zuwa safiyar yau. An gaya mana cewa sun kona dukkan kayayyakin jin kai kuma mutane da yawa suna mutuwa a garin, ”Bukar Alhaji Modu wanda ya gudu zuwa Gubio ya shaida
Da yake tabbatar da harin a baya, Shugaban karamar hukumar, Mustapha Bunu Kolo ya fada wa manema labarai cewa harin ranar Talata ya yi matukar barna yayin da ISWAP ta kwace garin.
“Duk da cewa ba na cikin Damasak, yayin da na fita domin yin aiki a hukumance, amma bisa ga bayanin da nake da shi, maharan sun mamaye garin tun karfe 5 na yamma kuma suna ci gaba da kasancewa har zuwa wannan lokaci (10:40 na dare).
”Maharan sun yi nasarar lalata sauran cibiyoyin jin kai, kasuwa, kantuna da kuma wasu gidaje da ba a tantance adadinsu ba, yayin da suka tayar da Bama-bamai (IEDs) ba tare da kalubalantar su ba.
Kolo ya ce “An kuma sanar da ni cewa mutane da yawa sun rasa rayukansu a harin, amma ba ni da hakikanin adadin wadanda suka rasa rayukansu yayin da maharan suke har yanzu, kuma suna ci gaba da yin barna a kan fararen hula marasa laifi,” in ji Kolo.
Dukkansu Kanar Ado Isa, mai magana da yawun rundunar Operation Lafiya Dole da Birgediya Janar Mohammed Yerima, Kakakin Sojojin ba su mai da martani ba game da sakonnin tes da aka tura musu kan harin da kuma zargin cewa sojoji kawai sun kare sansaninsu.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *