fbpx
Saturday, April 17
Shadow

Ana Kashe Biliyan N120 Akan Tallafin Man Fetir Duk Wata>>Mele Kyari, Babban Daraktan NNPC

Babban Manajan Darakta na Kamfanin Mai na Kasa (NNPC), Mele Kyari, ya ce a halin yanzu ana ba da tallafin man akan farashin tsakanin N100 zuwa N120 billion kowane wata.
Kyari ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis yayin gabatar da tambayoyi daga manema labarai na fadar gwamnatin jihar a karo na biyar na gabatar da bayanai daga ministoci na musamman da kungiyar sadarwa ta fadar shugaban kasa ta shirya.
Hakan na faruwa ne yayin da ake cece-kuce game da cire tallafin man fetur tsakanin gwamnatin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan da kuma gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta yanzu.
Ya ce kamfanin ba zai iya daukar ganin yadda ake sayar da man a yanzu kan N162 kan kowace lita ba.
Ya yi magana ne bayan karamin Ministan Albarkatun Man Fetur, Timipre Sylva, ya yi bayani a kan kokarin da ake yi na tabbatar da kudurin dokar Masana’antar Man Fetur (PIB).
Kyari, wanda ya ce kamfanin na NNPC yana shanye bambancin kudin da ke rubuce a cikin litattafan kudi, ya bayyana yayin da ainihin kudin shigowa da sarrafawa ya kai N234 a kowace lita, gwamnati na siyarwa kan N162 kowace lita.
Ya ce dole ne a bar al’amuran kasuwa su tantance farashin famfo na fetur a kasar.
Sai dai ya kara da cewa gwamnati na yin la’akari da yadda tasirin karin farashin ya shafi ‘yan Najeriya.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *