fbpx
Wednesday, January 26
Shadow

Ana sakin ‘yan Bindigar da aka kama ba tare da hukuntasu ba>>Gwamnan Zamfara

Gwamnan Zamfara, Bello Matawalle ya bayyana cewa, ana sakin ‘yan Bindigar da aka kama ba tare da hukuntasu ba.

 

Yace hakan na kawo koma baya wajan magamce matsalar tsaron dake damun Najeriya.

 

Gwamnan ya bayyana hakane yayi  da ya karbi bakuncin tawagar gwamnatin tarayya data jeyiwa mutanen jiharsa jaje kan kisan da ‘yan Bindiga suka yi a Bukkuyum da Anka.

 

Me baiwa shugaban kasa shawara kan harkar tsaro, Babagana Monguno,  shugaban ‘yansanda, IG Usman Baba Alkali, da ministan tsaro, Bashir Magashi ne tare da wasu sauran wakilai suka je jihar ta Zamfara.

 

Gwamna Matawalle ya kara da cewa,  jami’an tsaro na kokari amma suna fuskantar karancin kayan aiki musamman na zamani.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *