fbpx
Thursday, May 6
Shadow

Ana samun ƙaruwar yi wa yara fyaɗe a jihar Gombe

Masu fafutukar kare haƙƙin mata da ƙananan yara sun alaƙanta ƙaruwar cin zarafin mata da ake samu a jihar Gombe da jan ƙafar da ake yi a shari’o’in masu aikata lalata.

Wani bincike na baya-bayan nan ya ce Gombe na cikin jihohin da ke sahun gaba a Najeriya a yawan cin zarafin yara.

Haka kuma, an danganta ƙaruwar lamarin da rashin ƙwararan dokokin hukunta masu aikata laifin a jihar.

Kwamishinan ƴan sandan jihar Maikuɗi Shehu ya ce kusan kullum suna samun rahoton fyaɗe musamman na ƙananan yara.

Ya ce “sai ka ga dattijo ya lalata ƙaramar yarinya. Wannan ba ya rasa nasaba da shaye-shayen miyagun ƙwayoyi. Shi ya sa muke duba yadda za mu shawo kan wannan matsala”

Wata mai fafutukar kare haƙƙin,Hajiiya Fati Usman Kulani ta ce idan ba a yi wa tufkar hanci tun yanzu ba, nan gaba abun zai gagari kowa.

Ta kuma ce ana aikata waɗannan laifukan ne kan talakawa marasa galihu da ba za su iya ɗaukar nauyin shari’a ba.

“Sau da yawa waɗanda suka aika laifin sun fi iyayen yaran da aka lalata. Don haka sai a bar iyayen yara da zirag-zirga, ai da dage shari’ar har abin ya bi ruwa,” a cewarta.

Ta kuma ce iyayen yara su daina kunyar kai ƙara.

Sai dai a kwanan nan ne aka gabatar da wani ƙudiri a gaban majalisa wadda za ta sa a tsaurara hukunci ga masu cin zarafin ƙananan yara.

BBChausa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *