fbpx
Thursday, September 23
Shadow

Ana zargin wani mutum ya karya hakarkarin matarsa yayin da yake kokarin yi mata kaciya da filaya

An zargi wani mutum mai shekaru 54 da karya hakarkarin matarsa ​​mai shekaru 45 a lokacin da yake kokarin yi mata kaciya da filaya.

Lamarin ya faru ne ranar Talata 7 ga watan Satumba a Mombasa, Kenya kuma an gano cewa ma’auratan sun shafe tsawon shekaru 26 a tare.

Matar da ta bayyana cewa ta karya hakarkarinta yayin da take kokarin hana mijinta yi mata kaciya, ta ce sun yi fada jim kadan bayan ya isa gida da misalin karfe 5 na yamma kuma ya same ta a wajen gidan tare da sauran makwabta.

Wajen karfe 8 na dare, ta yi zargin cewa mutumin ya ja ta zuwa cikin gidan ya yi mata duka har ta suma. Matar ta ce, mijinta yayi mata tsirara sannan ya sanya filaya a cikin al’aurarta don yi mata kaciya, ba tare da sani ba.

A cewarta, wannan shine karo na biyu da mijinta ke kokarin yi mata kaciya kamar yadda yayi kokarin yin hakan a watan Agusta.

Sai dai mijinta ya musanta zargin, yana mai cewa matarsa ​​ce ta kai masa hari.

Yace; “Bai saka komai a al’aurarta ba, kuma zargin tana da wani mutum a wajen, sannan yanzu a shirye nake in sake ta tunda ba ta iya kula da yaranmu. ”

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *