fbpx
Tuesday, August 3
Shadow

Ana zargin ‘yansanda da kashe wani dan shekaru 33 a Jihar Bauchi

Ana zargin ‘yansanda da kashe wani dan kasuwa, Dauda Danladi a Unguwar Yelwa Kagadama dake jihar Bauchi.

 

Ana zargin ‘yansandan sun ganawa Dauda Azabane har ya mutu. Punchng ta ruwaito cewa dangi da abokan arziki na ta Alhinin rasuwar mamacin.

 

Dauya daga cikin wanda suka shaida lamarin, Laitu Nuhu, ta bayar da labarin cewa, ‘yansandan da Vigilante sun kama Dauda ne yayin da ake ta gaya musu cewa mutumin kirkine.

 

Saidai Kwamishinan ‘yansandan Jihar, Sylvester Alabi yace sun je kamene sai suka ga mutumin na numfashi sama-sama shine suka taimaka masa suka kaishi Asibiti, yace yanzu da kyaleshi sukayi za’a zagesu, kuma gashi sun taimakeshi ma ana cewa sun yi ba daidai ba.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *