fbpx
Monday, September 27
Shadow

APC ta lashe zaben shugabancin karamar hukumar Igabi

An ayyana Jabir Khamis na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban karamar hukumar Igabi da ke jihar Kaduna a ranar 4 ga watan Satumba.

Da yake sanar da sakamakon a ranar Lahadi a sakatariyar karamar hukumar Igabi, jami’in tattara sakamakon zaben, Dakta Mustapha Musa, ya ce Khamis ya samu kuri’u 29,804 inda ya doke babban abokin hamayyarsa, Dr Ibrahim Yusha’u na PDP wanda ya samu kuri’u 10,865.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa jam’iyyun siyasa 18 ne suka fafata a zaben.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *