fbpx
Monday, May 10
Shadow

Arewa ba ta jin tsoron sake fasalin kasa>>Gwamna Masari

Gwamnan jihar Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari ya yi watsi da jita-jitar cewa Arewa ba ta goyon bayan sake fasalin Najeriya.

A cewar jaridar ThisDay, Masari ya lura cewa hanyar da za a sake fasalin kasar ya kamata ya inganta daidaiton rarar mutane da albarkatun kasa.
“Wanene ya ce Arewa ba ta sha’awar sake fasalin kasar? Ina ganin Arewa ta yi amannar cewa ya kamata a rarrabar da mulki zuwa kasa-kasa. A cikin hakan, kun san abubuwa da yawa zasu zo da shi.
“Abin da nake fada maku ya fi ra’ayina na kashin kaina, domin kuwa ko da daga Kungiyar Gwamnonin Arewa, akwai amincewa a kan batun rarraba ikon mika mulki zuwa kasa-kasa. Abinda ya kamata shine ayi aiki dashi, “inji shi.
Masari, wanda kuma shi ne Shugaban Kungiyar Gwamnonin Arewa-maso-Yamma, ya sake nanata cewa raba iko zai cire rabuwar kokarin tarayya, jihohi da na kananan hukumomi ta fuskar samar da kayayyakin more rayuwa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *