fbpx
Thursday, December 2
Shadow

Ashe mawakin Amurka Lil Wayne dan Najeriya ne?

Wata jami’ar gwamnatin Najeriya ta yi maraba da mawakin nan dan kasar Amurka Lil Wayne bayan da ya ce gwajin kwayoyin halitta da ya yi ya nuna cewa kakaninsa ‘yan asalin Najeriya ne.

Mai taimaka wa Shugaba Muhammadu Buhari kan sha’anin ‘yan kasashen waje, Abike Dabiri, ta bayyana Wayne a matsayin “dan uwanmu dan Najeriya”.
Ms Dabiri ta ce tana fatan yi masa marhabin idan ya je Najeriya.
Wayne ya shaida wa gidan talbijin na Revolt TV cewa gwajin kwayoyin halittar ya nuna cewa kashi 53 na tsatsonsa daga Najeriya suke kuma yana fatan kai ziyara kasar.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *