fbpx
Tuesday, May 18
Shadow

Atletico Madrid ta baiwa Barcelona damar darewa saman teburin gasar La Liga bayan tasha kashi a hannun Athletic Bilbao daci 2-1

Atletico Madrid ta kara samun cikas a burinta na lashe kofin La Liga bayan Athletic Bilbao ta doke ta daci 2-1, yayin data baiwa Barcelona damar darewa saman teburin gasar a mako mai zuwa.

Bilbao ta fara jagorancin wasan ne cikin mintina tara ta hannun Alex Berenguer kuma kungiyar ta barar da damarmakin kara jagorancinta a wasan har Atletico ta rama kwallon ta hannun Stefan Savic a minti na 77.

Atletico Madrid ta cigaba da jajircewa domin tayi nasara a wasan amma a karshe Bilbao ce tayi nasara bayan dan wasanta na baya Inigo Martinez yaci mata kwallo da kai a minti na 86.

Har yanzu dai Atletico Madrid ce a saman teburin gasar La Liga da maki 73 amma Barcelona ta uku mai 71 ka iya wuce ta ta dare saman teburin gasar idan ta lallasa Granada a ranar alhamis.

La Liga leaders Atletico Madrid lost to Athletic Bilbao giving Barcelona the chance to go top

LaLiga leaders Atletico Madrid’s title bid was derailed again as they were beaten 2-1 at Athletic Bilbao, offering Barcelona the chance to go top of the table next week.

Alex Berenguer put the hosts ahead in the ninth minute and they missed a slew of chances to increase their lead before a Stefan Savic header pulled Atletico level in the 77th minute.

Diego Simeone’s pacesetters went for the winner but were caught out down the other end when Athletic defender Inigo Martinez headed home from a corner in the 86th minute.

Atletico still lead the table on 73 points but third-placed Barca, on 71 points, can go clear at the top if they beat Granada on Thursday.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *