fbpx
Wednesday, April 21
Shadow

Author: hutudole

Pantami Mutum ne me kima da tsare doka, wasu ne da basu son zaman lafiya ke Kiraye-kirayen saukeshi>>Wata Kungiyar Fafutuka a Legas

Pantami Mutum ne me kima da tsare doka, wasu ne da basu son zaman lafiya ke Kiraye-kirayen saukeshi>>Wata Kungiyar Fafutuka a Legas

Uncategorized
Wata kungiyar dake fafutuka kan rajin kare hakkin Bil'adama dake Legas ta bayyana goyon bayanta ga Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Zamani, Sheikh Isa Ali Pantami.   Kungiyar tace Pantami Mutum ne me bin doka da kuma Basira sannan yana daga cikin manyan jami'a gwamnatin Buhari.   Kungiyar me suna Coalition of civil society for good governance wadda hadakar wasu kungiyoyin fafutuka ce ta bakin Shugabanta, Declan Ihekaire ta bayyana cewa, kiraye-kirayen sauke Pantami, wasu manyan mutanene suka dauki nauyinsa wanda basu son zaman lafiya a Najeriya.   Kungiyar tace fitowar da Pantami yayi ya amsa cewa yayi waccan magana sannan yayi bayanin dalili, abun yabo ne wanda ba kowane zai iya ba, tace hakan ya nuna cewa Ministan nada gaskiya da kuma Kishin kasa. ...
EFCC sun Tsare tsohon Gwamnan Zamfara, Yari

EFCC sun Tsare tsohon Gwamnan Zamfara, Yari

Siyasa
Hukumar yaki da Rashawa da cin hanci, EFCC ta tsare tsohon gwamnan jihar Zamfara, Abdulaziz Yari a jiya, Talata.   Lamarin ya farune a Ofishin hukumar dake Sokoto.   An tsare Yari ne bisa zargin almundahanar wasu makudan kudi. Wata majiya daga hukumar EFCC ta bayyanawa Daily Trust cewa akwai yiyuwar a tsare tsohon gwamnan har nan da mako 1.
Ku binciki Pantami>>Kungiyar Kiristoci ta CAN ta gayawa DSS

Ku binciki Pantami>>Kungiyar Kiristoci ta CAN ta gayawa DSS

Siyasa
Shugaban Kungiyar Kiristoci ta Najeriya, CAN, watau Rev. Samson Ayokunle ya bayyanawa hukumar 'yansandan farin kaya ta DSS cewa, su binciki ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Zamani, Sheikh Isa Ali Pantami.   Da yakw magana a wajan taron cocin da aka yi a Ibadan, Samson ya bayyana cewa, shin wai me DSS suke yi?   Yace wanna ba abune da za'a daukeshi sakwa-sakwa ba. Saidai da aka tambayeshi konme yasa DSS din basu Binciki Pantami ba, ya bayyana cewa bai sa Dalili ba. “What is the State Security Service doing? What are the police doing? What is the Director-General of the National Intelligence Agency doing about the allegation? Such allegations should not be taken with levity. It should be taken seriously especially if we have data, written evidence, implicating ...
Farashin Man Fetur ya karu

Farashin Man Fetur ya karu

Kasuwanci
Farashin da ake baiwa 'yan kasuwa Man Fetur ya karu zuwa Naira 216.31 akan kowace Lita yayin da farashin danyen man ya tashi a kasuwannin Duniya. Hakanan faduwar darajar Naira ma ya taimaka wajan karuwar Farashin.   Shugaban kamfanin man fetur na kasa, Mele Kolo Kyari ya bayyana cewa farashin man fetur din ya kamata ya zama 211, zuwa 234, akan kowace Lita.   Yace amma gwamnati na amfani da Biliyan 120 duk wata wajan bayar da tallafi akan farashin man. A rahoton wanda Punchng ta a wallafa, Yawan Man fetur din da 'yan Najeriya kesha ya kai Lita 4.6bn
Najeriya zata dawo da Jakadiyarta ta kasar Ingila saboda baiwa ‘yan IPOB Mafaka

Najeriya zata dawo da Jakadiyarta ta kasar Ingila saboda baiwa ‘yan IPOB Mafaka

Siyasa
Akwai yiyuwar Gwamnatin tarayya ta dawo da jakadiyarta ta kasar Ingila saboda yanda kasar ta baiwa tsageran IPOB mafaka.   Kasar Ingila ta baiwa tsageran IPOB da gwamnati ke takurawa damar neman mafaka a kasarta. Hakan ya batawa gwamnatin Najeriya rai sosai inda Ministan Yada Labarai da Al'adu, Lai Muhammad ya bayyana hakan da yiwa yaki da Ta'addanci n da Najeriya ta ke zagon kasa.   'Yan IPOB dai na fafutukar ganin an baiwa Inyamurai kasarsu. Saidai ana zarginsu da kaiwa jami'an tsaro hare-hare.
Chelsea da Manchester City zasu fita daga gasar European Super League

Chelsea da Manchester City zasu fita daga gasar European Super League

Wasanni
Kungiyar Chelsea ta bayyana cewa zata fita daga gasar European Super League bayan da masoyanta suka gudanar da zanga zanga a wajen filin kungiyar gami da wasan su da Brighton a gasar Premier League.   Itama kungiyar Manchester City ta bayyana cewa bata so ta kasance a cikin gasar ta Super League ba, kuma zata fita daga gasar kamar ta bayyana a yammacin ranar talata.   A ranar lahadi ne kungiyoyi 12 suka kaddamar da wannan gasa wanda suka hada da Manchester City, Manchester United, Liverpool, Chelsea, Arsenal da Tottenham da dai sauran su. Kuma tun bayan gabatar da gasar ake ta cecekuce akan kafa ta.     Chelsea and Manchester City to leave European Super League Chelsea, whose fans protested against the planned breakaway league outside Stamford Bridge ahead of Tuesday's Prem...
Na kadu da Mutuwar Shugaban Chadi, Munyi babban Rashi>>Shugaba Buhari

Na kadu da Mutuwar Shugaban Chadi, Munyi babban Rashi>>Shugaba Buhari

Uncategorized
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana marigayi shugaban kasar Chadi Idris Deby da ‘jajirtaccen shugaba’, wanda mutuwarsa za ta bar gagarumin gibi a yakin da kasashen duniya ke yi da kungiyoyin ‘yan ta’adda. Yayin da yake bayyana kaɗuwa da kashe Idris Debby da ‘yan tawaye suka yi, Shugaba Buhari ya ce mutuwar shugaban mai shekara 68 za ta bar babban giɓi a ƙoƙarin hadin gwiwa da ake yi na murƙushe mayakan Boko Haram da kungiyar ISWAP. Sanarwar da fadar shugaban kasar ta fitar, ta Ambato Shugaba Buhari na cewa ‘Ina cikin alhini da kaɗuwa kan mutuwar Shugaba Idris Deby a fagen daga a ƙoƙarin da yake yi na kare kasarsa.’’ Shugaban Najeriyar ya jinjina wa marigayi Idris Deby a yaƙin da yake yi da kungiyar Boko Haram, ya kuma kira shi da ‘’babban abokin Najeriya. "Sannan ya sanya...
Tunda aka kafa Najeriya ba’a taba samun gwamnati kamar ta Buhari ba>>APC

Tunda aka kafa Najeriya ba’a taba samun gwamnati kamar ta Buhari ba>>APC

Uncategorized
Jam'iyyar APC ta bayyana cewa, tunda aka kafa Najeriya, ba'a taba samun Shugaban kasa kamar Muhammadu Buhari ba.   Sakataren Kwamitin Riko na jam'iyyar APC, John Edehe ne ya bayyana haka a wajan ganawa da manema labarai.   Yace amma masu sukar gwamnatib sun rufe ido basa fadar gaskiya. Yace babu gwamnatin data taba Talakawa kai tsaye kamar ta Shugaba Buhari.
Majalisar Tarayya na Shirin amincewa da kafa ma’aikatar kula da dabbobi

Majalisar Tarayya na Shirin amincewa da kafa ma’aikatar kula da dabbobi

Siyasa
Rahotanni sun bayyana cewa, Majalisar Dattijai na shirin amincewa da kafa wata hukuma da zata rika kula da dabbobi.   Kudirin dokar dan majalisa, Birma Muhammad Enagi ne ya kaishi zauren majalisar inda kuma tuni ya tsallake karatu na 2.   Dan majalisar yace idan aka kafa wannan hukuma, zata taimaka wajan hana yawo da dabbobi n zuwa guri-guri kuka zai taimaka wajan rage yawan satar Shanin.