fbpx
Tuesday, June 15
Shadow

Awanni kadan bayan gargadin da Gwamna Ganduje yayi, Yan Bindiga Sun Sace Wani Dan Kasuwa, Sun Harbe Wani Yaro A Kunne A Jihar Kano

Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun sace wani attajirin dan kasuwa a garin Kore na karamar hukumar Dambatta da ke jihar Kano.
A cewar wani shaidar gani da ido, lamarin ya faru ne da yammacin ranar Alhamis bayan wasu ‘yan bindiga sun mamaye garin.
An kuma tattaro cewa ‘yan bindigar sun kai hari kan mutane shida, kuma sun sace wani attajirin dan kasuwa. A yayin harin, rahotanni sun ce harsashi ya sami wani yaro a kunne.
Ba a iya gano halin da yaron yake ba har zuwa lokacin hada wannan rahoton.
Mazauna yankin sun ce lokacin da aka kai musu harin, babu wani jami’in tsaro da ya kawo musu dauki ko kuma suka zo wurin.
Sun ce mutane da yawa sun gudu cikin daji saboda harbin bindiga.
Shugaban karamar hukumar, Muhammad Abdullahi Kore, wanda ya tabbatar da afkuwar lamarin ya bayyana sunan wanda aka sace a matsayin Emmanuel, wanda ke gudanar da kasuwancinsa a garin Kore.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *