fbpx
Saturday, October 16
Shadow

Ba a kai wa ƴan sanda hari ba a Shinkafi>>Ƴan sandan Zamfara

Rundunar ƴan sandan jihar Zamfara a arewa maso yammacin Najeriya ta ƙaryata labarin da ke cewa ƴan bindiga sun kai hari ofishin ƴan sanda biyu a yankin Shinkafi.

A cikin wata sanarwa, kakakin rundunar ƴan sandan jihar SP Mohammed Shehu ya ce “babu wani hari da aka kai a ofishin ƴan sanda a ƙaramar hukumar Shinkafi ko wani yanki na Zamfara kamar yadda aka ruwaito.”

Sai dai sanarwar ta ce ƴan bindiga sun yi yunƙurin kai hari garin Shinkafi amma aka murƙushe su.

Rahoton wanda jaridar Daily Trust ta wallafa ya ce ƴan bindiga sun abka da magariba cikin garin Shinkafi suka kwashi makamai a ofishin ƴan sanda.

Samun cikakken rahoton abin da ke faruwa a Zamfara ya yi ƙaranci musamman a yankin na Shinkafi, kamar sauran jihar da aka katse hanyoyin sadarwa fiye da mako uku.

Wasu mazauna yankin da ke zuwa jihohi da ke makwabtaka da Zamfara na cewa abincin jama’a da dama ya kare ga kasuwanni na rufe, ga shi layukan sadarwa a toshe babu damar yin magana.

A cewar SP Shehu babu wanda aka kashe ko aka yi garkuwa da shi a yankin na Shinkafi.

“Babu wata matsala a halin tsaro a garin, inda al’ummomi ke gudanar da kasuwancinsu. Yayin da ake aiwatar da sabbin matakan tsaro yadda ya kamata,” in ji shi.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *