fbpx
Saturday, December 4
Shadow

Ba a Najeriya bane kadai, Farashin kayan abinci ya yi tashi mafi girma a duniya cikin shekara 10>>MDD

Farashin abinci a duniya ya yi tsadar da bai taba yi ba cikin shekara 10 bayan tashin da ya yi da kashi 30 cikin 100 a bara, in ji hukumar abinci ta Majalisar Dinkin Duniya (FAO).

Alƙaluman hukumar sun nuna yadda farashin hatsi da na kayan miya da mai ya yi tashin gwauron zabi a duniya.

Man da ake tatsa a jikin kayan miya ya tashi da kashi 10 cikin 100 a watan Oktoba.

Yankewar da aka samu wajen kai kayayyaki, da tashin farashin kayan amfanin yau da kullum, da rufe ma’aikatu da kuma rikicin siyasa, sun taimaka wajen tashin farashin.

FAO ta ce ma’aunanta sun nuna farashin hatsi ya tashi da sama da kashi 22 idan aka kwatanta da farkon wannan shekarar.

Farashin dawa na daya daga cikin wadanda suka taimaka wajen wannan hauhawa, inda ya karu da kashi 40 a wata 12 a baya, wannan kuma na da nasaba da rashin samun amfanin gona mai kyau da manyan kasahsen da suke fitar da shi suka yi irin su Rasha da Canada da Amurka.

“Kamar bangaren hatsi, za a iya cewa matsalar sauyin yanayi ce ta janyo kuma daga baya aka samu karancin amfanin gona,” kamar yadda Peter Batt, wani mai harkar kayan noma a makarantar koyar da kasuwanci ta Curtin, ya shaida wa BBC.

“Mun samu munanan shekaru na samun albarkacin noma a wurare da dama.”

FAO ta ce alkalumanta kan mai da ake tatsa daga kayan miya ya tashi ne sanadin tsadar manja da waken suya da sauransu.

Dangane da tsadar manja kuwa, farashin ya tashi ne sanadiyyar rage fitar da shi da ake yi daga Malaysia saboda karancin ma’aikata ‘yan cirani da aka samu, in ji FAO.

Karancin ma’aikata na taimakawa wajen tashin farashi da kuma tsadar kayan da ake hada kayan da su, kazalika da yadda ake kai kayan abinci wasu sassan duniya.

Mista Batt ya ce: ” Wata matsalar kuma ita ce yadda ake fitar da kayan da ake yi. Misali kamar a nan Australia, mun samu jirgin da zai zo ya dauki kayan abincin ya fita da su amma babu ma’aikatan da za su kwaso su saboda annobar korona.”

Matsalar da ake samu wajen kwasar kaya a jirgin ruwa ta tashi farashin madara, yayin da farashin ya karu da kashi 16 a bara.

Brigit Busicchia ta jami’ar Macquarie ta ce jita-jitar da ake yadawa a kasuwannin duniya ta taimaka wajen yin tangal-tangal din farashi.”Tun a shekarun 1990, janyewar gwamnati wajen gudanar da kasuwancin kaya ta sanya cibiyoyi da yawa da masu zuba jari sun shiga kasuwa da karfinsu.”

Wannan ya haifar da mummunan tasiri kan kasashen da suka dogara kan abincin da ake shigar musu da shi.

“Sai dai kasashe irin su Masar da sauran kasashen da suke yankin Gabas ta Tsakiya ba su fuskanci irin wadannan matsalolin ba,” in ji ta.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *