fbpx
Thursday, July 29
Shadow

Ba gudu ba ja da baya kan gwagwarmayar kafa kasar Biafra – IPOB

Kungiyar IPOB ta tabbatar da kamun Nnamdi Kanu, shugabanta, tana mai cewa ci gaban “ba shi ne karshen hanya ba”.

A wata sanarwa da aka raba wa manema labarai a ranar Laraba, Emma Powerful, mai magana da yawun kungiyar, ya bukaci mambobin IPOB da su “tattara” kuma su halarci zaman kotu a ranar 26 ga Yuli lokacin da za a ci gaba da shari’ar Kanu.

“IPOB ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen neman‘ yancin Biafra. Mun yi nisa a cikin gwagwarmayarmu na kafa Biafara. Babu gudu ba ja da baya duk kuwa da irin matakin tsoratar da mu da azzalumanmu suka yi, ”ya kara da cewa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *