fbpx
Tuesday, June 15
Shadow

Ba mataimakin Ikonso kuka kama ba, ya mana tsufa mu daukeshi aiki>>IPOB ga Sojoji

Kungiyar IPOB ta bayyana cewa, mutumin da Sojojin Najeriya suka kama da cewa membansu ne, Mataimakin Ikonso ba gaskiya bane.

 

Kungiyar ta bakin kakakinta, Emma Powerful ta bayyana cewa, mutumin yayi tsufa su daukeshi aiki cikin jami’ansu na ESN.

 

Ya kara da cewa babu dalilin da zai hana su amsa cewa membansu ne idan da gaskene, yace lokacin da aka kashe Ikonso, sun fito sun amsa dan su basa karya kamar jami’an Najeriya.

 

Ya kuma kara da cewa sun gano cewa, Mutumin da aka kama, Basaraken garinsa ne ke da matsala dashi, shine ya masa cinne yace dan IPOB ne, saidai yace duk abinda za’a musu ba zasu daina fafutukar kafa kasar Biafra ba.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *