fbpx
Monday, November 29
Shadow

Ba Mu Da Hannu Cikin Kafa Raundunar Shege-Ka-Fasa, Kuma Ba Ma Tare Da Su, Cewar Gwamnonin Arewa

Kungiyar Gwamnonin Arewa ta nesanta kanta da kafa rundunar tsaro ta Shege ka fasa. Kungiyar ta bakin shugaban ta Gwamnan Filato, Simon Lalong ne ya shaidawa manema labarai a jiya.

Gwamnan ya ce Kungiyar Gwamnoni ba ta san an kafa wata Shege-Kafasa ba kuma basa tare da ita.
Ya ce “hakika mun ji cewa an kafa rundunar, amma  kungiyar ba ta daga cikin wadanda suke son samar da waccan runduna ta Shege Ka Fasa”.
Sai dai a martaninsa, Shugaban waccan Runduna Abdulaziz Suleiman a jiya Lahadi ya bayyanawa manema labarai cewa matakin da suka dauka ba ya bukatar tuntubar Gwamnonin na Arewa.
Kawai dai sun dauki matakin ne domin tabbatar da ganin cewa an magance kalubalen tsaro a  yankin na Arewa sannan kungiyar ta tabbatar da cewa tana kan matsayinta na ganin cewa ta gabatar da abubuwa yadda ya kamata tare da kakkabe kalubalen da al’umma suke fahimta a yankin Arewa.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *