Gwamnatin Jihar Neja ta ce ba ta da tabbacin lokacin da za a sake bude makarantun boko da aka rufe sakamakon matsalar rashin tsaro da ta addabi jihar.
Kwamishiniyar Ilimi ta jihar, Hon Hannatu Jibrin, ce ta fadi haka yayin haduwa tare da mika daliban Kagara da aka sace ga iyalansu a ranar Lahadi.
A cewar Kwamishinan, gwamnati na ganawa da iyaye, malamai da sauran masu ruwa da tsaki domin fito da wani tsari na sake bude makarantun