fbpx
Monday, November 29
Shadow

‘Ba mu hana likitoci duba masu harbin bindiga ko hatsarin mota ba’

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta ce ba ta taba cewa wani asibiti a kasar kada ya duba mutanen da suka je neman lafiya da harbin bindiga, har sai ya samo izini daga gare ta ba.

Babban Sufeton ‘yan sandan kasar Alkali Baba ne ya bayyana haka, yayin wani taron tattaunawa don gano hanyoyin aiki da dokar da ta tilasta duba wanda aka harba da bindiga a asibiti, wanda kungiyar lauyoyin kasar ta shirya.

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta nuna rashin jin dadi a kan laifin da ta ce ana ɗora mata babu gaira babu dalili.

Babban Sufeton ‘yan sandan wanda mai magana da yawun rundunar Mista Frank Mba ya wakilta ya ce, ‘yan sanda ba su taɓa hana likitoci duba mutumin da aka harba ko wanda ya yi hadari ko wanda aka cakawa wuƙa a asibiti ba, hasali ma suna aiki ne kafada-da-kafada da likitoci wajen kare rayukan al’umma.

Frank Mba ya kara da cewa; ”Likitocin Najeriya ba sa bukatar ko wanne irin rubutu daga ‘yan sanda kafin su fara duba wadanda aka harba da bindiga ko wadanda suka yi hadari a titi.

Suna da ‘yancin duba mutanen da zarar an kai su asibitin da ke kansu da muka bukaci su sauke shi ne lokacin da suke duba mutum suka ga harbin bindiga ne to su yi saurin kiranmu,” inji Mista Mba.

Dr Idris shi ne kakakin kungiyar asibitocin kudi na Najeriya a Abuja, ya ce, ”baya ga batun samun sahalewar ‘yan sanda akwai kuma batun kudi.

Watakila wani bangare na dalilin da ya sa ake jayayya tun shekarar 2017, shi ne yi wa mai raunin harbin bindiga magani ba kamar yi wa mai zazzabin cizon sauro magani ba ne.”

ya kara da cewa , ”Zai iya yiwuwa wanda aka harba ya ji wani ciwo na daban, baya ga harbin da aka yi masa kamar samun matsala a lakarsa, wanda sai an tattaro tawagar likitoci sannan a yi masa magani.

Kuma yawancin irin wadannan marassa lafiyar na zama asibiti sama da wata guda, shin wanene zai biya musu kudin asibitin?”

Majalisar tarayyar Najeriya ta amince da dokar duba lafiyar masu raunukan bindiga a 2017, don kawo ƙarshen mace-macen da ake samu na mutanen da suka ji rauni irin na bindiga ko wuƙa ko hadarin mota, saboda ƙin karɓarsu a asibitoci har sai sun samo rahoton ‘yan sanda.

Sai dai, duk da wannan doka, lauyoyi a Najeriya sun ce masu raunukan bindiga na ci gaba da shan tasku da kuma ƙin yi musu magani.

Sanata Shehu Sani tsohon ɗan majalisar dattijai wanda a lokacinsu ne aka ƙirƙiro wannan doka ya ce, akwai bukatar jihohi su samar da irin wannan doka don tabbatar da aiki da ita.

Ya kara da cewa: ”A wasu lokutan likitocin na tsoron karbar marassa lafiyar ne saboda kar ‘yan sanda su ce sun bai wa mai laifi mafaka ko kariya ko kuma taimaka musu.”

Ƙungiyar lauyoyin da ta shirya tattaunawar dai ta nanata cewa duk dan Najeriya, yana da hakkin ya rayu, ko da yana kan gargarar mutuwa ne duk da raunin da ya ji kamar na harbin bindiga.

Kasancewar ba a san hakikanin me ya yi masa rauni ko ta yaya ya ji raunin ba a lokacin, babu hujja wani likita ko asibiti ya ƙi duba lafiyar mutum, kuma hakan bai hana wani jami’in tsaro ko dan sanda taimaka wa mutumin da ya jikkatan zuwa asibiti don samun lafiya ba.

Masu kare haƙƙin ɗan’adam dai na da ra’ayin cewa lokaci ne kawai zai nuna ko iƙirarin ‘yan sanda na cewa sun daina tsangwamar duk wani likita don kawai ya ceto ran wani mai raunin harbin bindiga, kafin sanar da su daga bisani, zai tabbata ko kuma a’a.

Yayin da likitoci ke cewa maganar kuɗin aiki ga masu irin wannan rauni, wanda a wasu lokuta kan kasance maƙudai, shi ma wani abu ne da zai ci gaba da zama ƙadangaren bakin tulu ga dokar duba lafiyar masu raunukan bindiga ta 2017.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *