fbpx
Sunday, April 18
Shadow

Ba mu muka kaiwa hedikwatar ‘yansanda hari ba, ba halayyar mu bace>>Tsageran IPOB

Haramtacciyar Kungiyar dake son kafa kasar Biafra ta IPOB ta bayyana cewa, ba halayyar ta bace kaiwa jami’an gwamnati da hukumomi hari ba.

 

Hakan ya fito ne daga sanarwar da kakakinta Emma Powerful ya fitar yana kare kungiyar bisa zargin da ake musu na cewa sune suka kaiwa hedikwatar ‘yansanda da ta Hukumar gyara hali a Owerri jihar Imo hari, wanda hakan yai sanadiyyar guduwar masu laifi kusan 2,000.

 

Yace basu da hannu a lamarin. Yace an kafa kungiyar tasu ne dan zaman lafiya ka bata canja ba akan hakan. Yace jami’an tsaron su, ESN na can daji suna korar Fulani makiyaya to ta yaya za’a alakantasu da wadancan hare-hare?

“The attention of IPOB has been drawn again to the fallacious and fabricated news that IPOB and ESN are involved in the attack of prison and police headquarters in Owerri Imo State.

“IPOB and ESN are known groups not unknown gunmen. ESN is in the bush chasing Fulani terrorists, why linking IPOB and ESN to this attack. IPOB and ESN were not involved in the attack in Owerri Imo State. and the recent attack on Onitsha Owerri road at Ukwuorji junction. It is not our mandate to attack security personnel or prison facilities.

“The Nigeria Government and her compromised media outfits should stop linking IPOB and ESN to the multiple attacks going on in Nigeria now. IPOB was formed on principle of peace and we are still in it. Unknown gunmen is a different people which we don’t know them and they not IPOB or ESN security outfit.”

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *