fbpx
Thursday, December 2
Shadow

Ba Mu Yi Nadamar Zaben Buhari Ba>>Kungiyar Izala

Ba Mu Yi Nadamar Zaben Buhari Ba, Cewar Kungiyar Izala
Daga Comr Abba Sani Pantami
Kungiyar jama’atu izalatul bidi’a wa ikamatus sunnah dake da hedikwata a garin Kaduna, ta bayyana cewa ko kadan ba ta yi da na sanin zaben Shugaban Kasa Muhammad Buhari ba.

Shugaban kungiyar na Kasa Sheikh Abdullahi Bala Lau ne ya bayyana hakan ta cikin shirin Barka da Warhaka na Gidan Rediyon Freedom na jihar Kaduna a yau Talata.
Sheikh Bala Lau ya kara da cewa shugaba Buhari ya ba su damar ganawa da shi, kuma sukan tattauna matsalolin da suka shafi al’umma saboda hakan ne ya sanya ba a jin su suna fitowa kafafen yada labarai kan Gwamnatin Shugaba Buhari.
Idan za ku iya tunawa dai kafin zaben shekarar 2019 da ya gabata, Kungiyar Izala ta bukaci dukkannin mabiyan ta da su kada kuri’arsu ga dan takarar Jam’iyyar APC Muhammad Buhari.
Sheikh Bala Lau ya nuna takaicinsa kan jama’ar da ba su nuna uzirin su ga Gwamnatin shugaba Buhari, inda ya ce a kasar nan an samu ‘yan siyasar da suke wulakanta Al-qur’ani saboda siyasa, sannan an samu yaron da ya hada a baki aka sace shi da zummar karbar kudin fansa wajan mahaifinsa,
Sheikh Bala Lau ya kara da cewa Allah ba ya sauya wa mutane har sai sun sauya halayensu.
Sannan ya kara da cewa ga masu mummunan fata ga Gwamnati kuwa, tamkar mota ce ta dauko kowa, sai ku dinga mummunan fata ga direban, kunga abun zai fara rincabewa ne ya shafi kowa da kowa.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *