fbpx
Tuesday, June 15
Shadow

Ba Na Nuna Kabilanci Wajen Rabon Mukammai, Cancanta Nake Dubawa>>Shugaba Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa kwata-kwata shi idan zai nada mukamai, to cancanta ya ke dubawa, amma ba kabilanci ko bangaranci ba.

 

Buhari ya yi wannan bayani a cikin wata tattaunawa da shi da aka da Gidan Talbijin na Arise TV a ranar Alhamis.

 

Buhari dai kusan duk lokacin da ya nada mukamai sai ya sha suka cewa ya na nuna Arewanci, bangaranci ko kabilanci.

 

To amma kuma a cikin wannan tattaunawar, Buhari ya ce ga dahir ya na gani mutum ya cancanta, ba zai iya tsallake shi ya saki reshe ya kama ganye ba.

 

Saboda haka Buhari ya ce cancanta ya ke bi ba kabila ba.

 

Duk da haka akwai masu ganin cewa Buhari ba ya bin abin da dokar kasa ta ce, wato a raba mukamai ba tare da wani yanki ya yi korafin an maida ahi saniyar-ware ba.

 

Da ya ke magana kan mukamai, ya ce ba zai iya yin alfarma ga wadanda ba su dade a aiki ba, alhali ga wadanda su ka dade su na aikin.

 

“Mutane da yawa sun shafe ahekaru da yawa su na samun horo. Wasu sun yi shekaru 18, wasu fiye da 10. Sun samu horo a Zaria da Abeokuta. Sun bi matakan aikin soja mukamai daki-daki. To kuma ka na da irin wadannan kwararru kuma gogaggu, sai ka tsallake su ka dauko wani can da bai dade ba, bai kuma goge ba, don kawai a ga ka na raba-daidai a mukamai?” Inji Buhari.

 

Buhari na magana ne a kan nada sabon Babban Hafsan Askarawan Najeriya, Yahaya Faruk.

 

Na nada Yahaya sabon babban hafsan sojoji saboda yafi sanin dabarun yaki, kuma dakaru na goyon bayan sa.

Rariya.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *