fbpx
Sunday, September 26
Shadow

Ba ni da abin boyewa – Saraki yayi magana akan ‘kamun da EFCC ta mashi’

Bukola Saraki, tsohon Shugaban Majalisar Dattawa yayi magana kan gayyatar da Hukumar Yaki da Yiwa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) ta yi masa akai -akai, inda ya bayyana cewa a matsayinsa na dan kasa mai ‘yanci, ba shi da abin da zai boye.

Saraki a cikin wata sanarwa ta hannun mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Yusuph Olaniyonu ya ce ya ziyarci ofishin hukumar ta EFCC bisa son ransa don fayyace batun da hukumar za ta iya bijiro da shi.

Ya bayyana cewa ba a kama shi ba amma ya ba da kansa don nuna cewa ba shi da abin da zai ɓoye.

Rahotanni sun yi ikirarin cewa an kama Saraki ne bisa laifin zamba.

Duk da haka, Saraki a cikin sanarwar ya rubuta: “Za a tuna cewa bin umurnin Babbar Kotun Tarayya, Abuja, kan karar Hakkin Dan Adam da Dakta Saraki ya shigar a lokacin tsohon shugaban EFCC wanda ya hana hukumar daga binciken sa har sai an kawo karshen lamarin, hukumar a zaman ta na karshe a ranar 14 ga Yuli, 2021, ta roki alkali cewa umurnin yana hana su yin aikin su.

“Bayan wannan korafi, Dakta Saraki, a matsayinsa na dan kasa mai amana, a bisa son ransa ya tunkari hukumar EFCC cewa a farkon lokacin da ya dace, a shirye yake ya ziyarci ofishin hukumar tare da fayyace duk wasu batutuwa da za su iya tasowa tare da shi.

“Don haka, ya ziyarci ofishin hukumar a ranar Asabar (31 ga Yuli) da rana kuma ya amsa wasu tambayoyi.

“Ya dawo gida. Ba a kama shi ba,”

Saraki ya kuma tabbatar wa EFCC cewa ba shi da abin da zai boye kuma a koyaushe zai ba da kansa don fayyace duk wani lamari da ka iya bukatar hankalin sa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *