fbpx
Thursday, August 5
Shadow

Ba ni da burin shiga siyasa – Tsohon sarkin Kano, Sanusi

Tsohon Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya karyata duk wani shiri na shiga siyasa.

Sanusi, wanda ke magana a Kaduna, ya ce yana shirin ci gaba da fadakar da jama’a kan ‘yan takara da shugabanni na gari da za su zabi yayin zaben.

Ya kuma bayyana cewa ya kamata a ba ilimi muhimmanci, musamman ga yara, kafin a shawo kan matsalolin kasar.

Sanusi ya musanta rashin jituwa da Dahiru Bauchi game da nadin shugaban darikar Tijjaniyya na Islama.

Sanusi ya ce; “Idan muna da wadanda muka amince da su wadanda suka yi alkawarin za su yi aiki don ci gaban kasar, to za mu iya haduwa mu taimaka musu – wannan ba siyasa ba ce. Ba ni da niyyar shiga siyasa.

“Idan ba mu ilmantar da yaranmu don su zama masu nasara ba, yayin da wasu mutane ke tura ‘ya’yansu makarantu, za su kare aiki ga wadanda suka halarci makarantar kuma karshen kenan.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *