fbpx
Monday, November 29
Shadow

Ba sai an roki Buhari ba, dolema ya saki Nnamdi Kanu, Kungiyar IPOB nawa Dattawan da suke je rokon Buhari ya saki Kanu Barazana

Wata kungiyar dake ikirarin kare muradin Inyamurai ta, Nzuko Ndigbo ta bayyana cewa, bafa sai an rika rokon Buhari ya saki Nnamdi Kanu ba.

 

Ta caccaki shugaban kasar kan kalamansa bayan ziyarar da dattawan Inyamurai suka kai masa fadarsa dake Abuja inda yake cewa zai duba yiyuwar sakin Kanun.

 

Kungiyar tace, Buhari bai yiwa Inyamurai Alfarma ba dan ya saki Nnamdi Kanu, dama can abinda ya kamata yayi ne.

 

Saidai kuma tace Boko Haram da Fulani masu sace mutanene ya kamata Shugaban ya mayar da hankali akai.

 

Hakanan rahotanni sun bayyana cewa, matasan Inyamuran sun saka kafar wando daya da sarakunan da suka je neman shugaba Buhari yawa Kanun Afuwa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *