fbpx
Wednesday, October 20
Shadow

Ba Za Mu Amince Da Tallata Batsa a Kano Ba>>Hukumar Tace Fina Finai

Ga duk mai bin wasu titina a birnin Kano zai ga allunan talla (signboard) dake dauke da katon hoton wata matsiraiciyar mace da kuma kananan hotunan ledojin omo na kamfanin *”Viva”*, wadanda sai ka lura sosai sannan ka gan su, wanda hakan ya saba da addini da tarbiyya da kuma al’adar al’ummar jihar Kano.

A daidai lokacin da Hukumar Tace Fina-finai da Dab’i ta jihar Kano ta sami labarin bullar wadannan hotunan batsa ne, shugaban hukumar Malam Isma’il Na’abba Afakallah ya umarci Jami’an hukumar (operation team) karkashin jagorancin malam Nazifi Aminu domin su gaggauta daukar matakin rufe hotunan da kuma gayyato wadanda ke da alhakin sanya wadannan munanan hotunan batsa.


Hukumar tana kira ga masu aikata irin wannan mummunan aiki da su daina saboda hukumar ba za ta zuba ido ta nade hannu ba tana kallo ana yada fasadi a tsakanin al’umma ba sannan hukumar tana kira ga daukacin al’umma da su ba ta hadin-kai wajen sanar da ita wajajen da ake kafa fastoci ko allunan tallace-tallace masu dauke da hotuna ko kalaman batsa, da ma masu yawo da lasifika suna tallan magunguna da kalaman batsa wadanda suka saba addini da tarbiyya da kyawawan al’adun al’ummar jihar Kano.

Daga Salihu Adamu Aliyu

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *