fbpx
Thursday, May 6
Shadow

Ba za mu koma Kasuwar Shasha ta Ibadan ba ​​- Waɗanda Rikicin Yarbawa da Hausawa ya Shafa

Wasu da rikicin ya rutsa da su a kasuwar Shasha da ke karamar hukumar Akinyele a jihar Oyo sun ce za su yi watsi da duk wani yunkurin gwamnatin jihar na mayar da su yankin don ci gaba da kasuwancinsu.

A cewar wadanda abin ya shafa, filin kasuwar bai ishe su damar yin kasuwanci ba kuma Yarbawa masu masaukin su suna kuntata masu.

Da yake zantawa da manema labarai, Shugaban kungiyar’ yan kasuwar Shasha, Alhaji Usman Nyako, ya ce ya gano wata kasuwar a yankin Iroko da ke kauyen Akinyele tare da isasshen fili don sauke dubban tirela.

Wata daga cikin wadanda lamarin ya shafa ta ce, “Sararin da ke Shasha ba zai iya daukar fiye da manyan motoci 90 a lokaci guda ba.”

Haka ma wani dattijo mai suna Abubakar Muhammed wanda ya fito daga karamar Hukumar Shanga a Jihar Kebbi, ya ce tun shekarar 1983 yake sayar da tumatir a Shasha.

Muhammed ya yi tir da yadda gwamnati ke tafiyar da lamarin, yana mai cewa, mun ga mutuwa amma Allah ya kubutar da mu, ban tunanin akwai mai hankalin da zai iya komawa Shasha, ni kam, ba zan koma ba.

Da yawa daga cikinmu Mutane kuma sun yanke shawarar ba za su koma can ba.

Ban gina gida ba amma kayana da suka lalace sun kai kimanin Naira miliyan biyu.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *