fbpx
Thursday, December 2
Shadow

Ba za’a yi zabe a Anambra ba idan ba’a saki Nnamdi Kanu ba>>IPOB ce zasu yi zaman gida dole na sati daya

Kungiyar IPOB ta bayyana cewa ba zata bari a yi zabe a Anambra ba idan ba’a saki shugabanta, Nnamdi Kanu ba

 

Kungiyar ta saka fokar zaman gidan dole ta tsawon kwanaki 7 wanda zata fara daga ranar 5 ga watan Nuwamba.

 

Kakakin IPOB, Emma Powerful ya bayyana cewa, sun dauki wannan mataki ne dan tursasa gwamnati ta saki shugaban nasu.

 

Saidai a bangarenta, Kungiyar kare muradun Inyamurai ta Ohanaeze Indigbo ta bayyana cewa, Zaben na da muhimmanci kuma bai kamata a hanashi ba.

 

Kakakinta, Alex Ogbonnia ya bayyana cewa, zaben na da muhimmanci sosai dan kuwa jihar itace cibiyar kasuwancin jihohin Inyamurai.

 

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *