fbpx
Saturday, June 19
Shadow

Ba Zai Yiwu A Ga Jinjirin Watan Shawwal A Nijeriya A Ranar Talata Ba>>Kwamitin Duban Wata

Kwamitin duban wata na majalisar koli ta shari’ar Musulunci a Nijeriya ya sanar da cewa ganin jinjirin watan Shawwal ranar Talata, 29 ga watan Ramadan zai yi wahala.

A bayanin da kwamitin yayi ranar Asabar a shafinsa na Facebook, ya bayyana cewa an yi hasashen ko wata ya bayyana zai fito ne gabanin faduwar rana, saboda haka ba zai yiwu a ga jinjirin wata ba ranar Talata a Najeriya. Amma duk da haka jama’ar Musulmi a fadin Najeriya su fita neman jinjirin wata saboda yin hakan ibada ne.

Ranar Talata, 11 ga Mayu ya yi daidai da 29 ga watan Ramadana da ake fara neman jinjirin watan Shawwal na shekarar 1442AH.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *