fbpx
Saturday, June 19
Shadow

Ba zamu bari a shigo da Masara daga kasar waje ba>>CBN

Gwamnan babban bankin Najeriya, CBN, Godwin Emefiele ya bayyana cewa ba zasu amince a shigo da masara daga kasar waje Najeriya ba.

 

Yayi maganar ne wajan kaddamar da noman Shinkafa na shekarar 2021 a Katsina a yau, Alhamis.

 

Bankin ya kuma jawo hankalin matasa da su rungumi noman Masara inda yace a shirye suke su talkafawa matasa akan lamarin.

 

 

Ya bayyana cewa kuma ba zasu amince a shigo da Masara daga kasar waje Najeriya ba, saboda manoman Masarar zasu iya samar da bukatun ‘yan Najeriya na Masarar na Tan Miliyan 4.5

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *