fbpx
Saturday, October 16
Shadow

Ba zamu shiga yakin Iran da Amurka ba amma idan Iran ta tabamu zata ji ba dadi>>Kasar Israila

Firaiministan kasar Israila,Benjamin Netanyahu ya bayyana cewa kasarshi ba zata shiga yakin da kasar Amurka ta jawo ba da kasar Iran, ya bayyana cewa harin da Amurkar ta kai wanda kashe Sojan Iran ita kadai ta kaishi dan haka babu ruwan kasarshi da wannan harka.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Rahoton Daily Mail ya kara da cewa, Netanyahu duk da a farkon harin ya yabawa kasar Amurka amma daga nan ya hana jami’an gwamnatinshi yin magana da ‘yan jarida akan wannan batu.

Saidai wani rahoton kuma na kamfanin dillancin labaran AFP na cewa Natenyahu ya gargadi kasar Iran da idan ta sake ta tabasu to fa zata ji ba dadi dan kuwa zasu kai mata harin ramuwar gayya me matukar muni.

Rahotanni dai sun bayyana cewa Israila na daya daga cikin kasashen da Iran zata kaiwa hari a matsayin ramuwar gayyar kisan kwamandan sojanta da aka yi.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *