fbpx
Saturday, April 17
Shadow

Ba zamu yafewa Najeriya ko sisi ba sai ta biyamu kudin data ci bashi>>IMF

Hukumar bada Lamuni ta Duniya, IMF ta cire Najeriya daga cikin jerin kasashen da zata yafewa bashin da take bi.

 

Zuwa yanzu Hukumar ta ware wasu kasashe 28 da zata yafewa bashin, inda za’a yi amfani da wasu kudi da aka ajiye na ko ta kwana wajan biyawa wadanna kasashen bashin da hukumar ke binsu.

 

Kasashen da aka yiwa yafiyar dai sune, Afghanistan, Benin, Burkina Faso, Burundi, Central African Republic, Chad, Comoros, Democratic Republic of the Congo, Djibouti, Ethiopia, da The Gambia. Sai kuma Guinea, Guinea-Bissau, Haiti, Liberia, Madagascar, Malawi, Mali, Mozambique, Nepal, Niger, Rwanda, São Tomé and Príncipe, Sierra Leone, Solomon Islands, Tajikistan, Togo da Yemen.

 

Jimullar bashin da za’a yafe musu shine dala Miliyan 238.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *