fbpx
Saturday, December 4
Shadow

Ba zan goyi bayan Buhari kan ta-zarce ba>>Shekarau

Tsohon gwamnan Kano, Ibrahim Shekarau, ya ce ba zai goyi bayan shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ba idan ya nemi karin wa’adi karo a uku.

Shugaba Buhari dai ya sha musanta zargin da wasu ‘yan kasar, musamman ‘yan jam’iyyar hamayya ta PDP, ke yi cewa yana so a yi wa kundin tsarin mulkin kasar kwaskwarima domin ya ci gaba da mulki kar na uku.
Sai dai a tattaunawarsa da BBC kan kudurin da majalisar dattawan kasar ta amince da shi na bukatar gyaa ga kundin tsarin mulkin kasar, Sanaa Shekarau ya ce ba ya tsammanin Shugaba Buhari zai nemi yin ta-zarce saboda kaunarsa ga mulkin dimokradiyya.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

“Ni dai a iya sanina ban san asalin wannan magana [yunkurin ta-zarcen Buhari ba]; idan ma akwai ta ni ban ji ta ba, ba a yi da ni ba…ko da irin wannan batu zai zo ina daga cikin sahun gaba da za su ce basu yarda ba.”

Tsohon gwamnan na Kano ya bukaci ‘yan kasar su kyautatawa Shugaba Buhari zato, yana mai cewa “yadda nake kyautata wa Janar Buhari zato ko da mafi kusancinsa sun kawo masa irin wannan tunani, ga hange na ba najin zai karbi wannan tsaro.”

A cewarsa, idan Buhari ya nemi yin ta-zarce hakan zai haifar da fitina a kasar.

Ba zan nemi karin wa’adi ba

A baya dai fadar shugaban Najeriya ta musanta rahotannin da ke cewa Shugaba Buhari na duba yiwuwar neman ta-zarce.

A wancan lokacin, kakakin shugaban kasar, Malam Garba Shehu ya tabbatar wa BBC cewa Shugaba Buhari ba zai sake tsayawa takara ba.

Kazalika a sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter ya bayyana cewa shugaban yana kaunar mulkin dimokradiyya ne, don haka ba zai taba yunkurin tsawaita mulkinsa ba.

“Abu ne mai muhimmanci a gane cewa a baya an yi yunkurin sauya kundin tsarin mulki, domin shugaban wancan lokaci ya yi wa’adi na uku. Hakan ba daidai ba ne kuma ya saba wa kundin tsarin mulki, kuma gara da aka dakile yunkurin.

“Babu wani yanayin da zai sa shugaba Buhari ya nemi gyara kundin tsarin mulki don sauya wa’adi biyun da yake da na zama shugaban kasa,” in ji Malam Garba Shehu.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *