fbpx
Thursday, July 29
Shadow

Ba zan yi ritaya daga siyasa kamar Masari ba, zan cigaba har ma bayan 2023 – Ganduje

Gwamna Umar Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya ce bai yi ritaya daga siyasa ba kamar Gwamna Aminu Bello Masari na jihar Katsina kuma zai ci gaba da aiki har bayan 2023.

Gwamna Ganduje ya fadawa manema labarai cewa tasirin sa na siyasa ba zai iya raguwa a cikin ‘yan shekaru ba tunda har yanzu yana nan kan aiki da tsarin.

“Burina na Siyasa ya wuce 1970s kuma zan ci gaba da kasancewa cikin siyasa har ma bayan 2023 ba zan yi ritaya ba saboda ban gaji da tsarin ba gaba daya”.

Ganduje ya nuna alamun cewa ba zai iya bayyana sarai abin da ko wane matsayi yake so ba, “amma bari in tabbatar muku cewa zan ci gaba da aiki saboda abin da nake yi kenan tun farkon shekarun 70s”.

A lokacin da yake amsa tambayoyi kan wanda zai gaje shi bayan 2023, Gwamnan ya ki cewa musamman ga wadan zai goyawa baya amma ya ba da tabbacin cewa wakilan da za su zabi mutum na gaba za su yi aiki tukuru.

Gwamna Umar Ganduje ya kuma lura cewa Najeriya na matukar bukatar sasantawa cikin rikice-rikice da dama kuma saboda haka ya kamata dukkan hannaye su kasance a kan abubuwa domin kyautatawa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *