fbpx
Sunday, September 19
Shadow

Babban Bankin Najeriya ya raba bashin biliyan N756.5 ga manoma miliyan 3.7

Babban Bankin na Najeriya ya bayyana cewa ya raba jimlar biliyan N756.51 ga sama da manoma miliyan 3.7 a karkashin shirin na Anchor Borrower’s tun lokacin da aka fara shirin a 2015.

Babban bankin ya bayyana wannan ne a cikin sanarwar sa mai lamba No. 137 na taron Kwamitin Manufofin Kudi Wanda ya fito a ranar Talata.

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya kaddamar da ABP a shekarar 2015 a wani yunkuri na bunkasa noman rani da kuma juyawa kasar nan gaba game da harkokin abinci da noma.

Wadanda suka ci gajiyar wannan shirin sun hada da manoma da ke noman hatsi (shinkafa, masara, alkama da sauransu) auduga, saiwa da doya, dawa, da wake, tumatir da dabbobi.

Sanarwar ta ce, “A karkashin tsare-tsaren kudi na ci gaban bankin, bankin ya bayar da biliyan N756.51 ga kananan manoma 3,734,938 da ke noman hekta miliyan 4.6, inda aka kara N120.24bn na daminar 2021 zuwa manoma 627,051 na hekta 847,484, a karkashin Shirin.

Babban bankin na CBN ya kuma bayyana cewa, ya zuwa yanzu, an raba kudi N121.57bn ga masu cin gajiyar 32,617 a karkashin shirin sa hannun jari na harkokin noma na kanana da matsakaita masu sana’a, shirin da MPC ta gabatar a watan Fabrairun 2017.

Ya kara da cewa ya zuwa watan Mayu 2021, kimanin SMEs 109,879 sun ci gajiyar shirinta na Kudin Karfafawa da kuma Asusun Ba da Jarin Matasa na Kasa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *