fbpx
Tuesday, June 15
Shadow

Babban Lauyan Tarayya, Malami, ya keta dokar hana amfani da shafin Twitter yayin da ya shiga goge shafinsa

Babban Lauyan Tarayya (AGF), Abubakar Malami, ya karya dokar da gwamnatin Najeriya ta yi na hana amfani da Twitter.

Gwamnatin Najeriya ta dakatar da Twitter a ranar Juma’ar da ta gabata bayan da Manhajar ta goge wata magana da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi, inda ya yi tsokaci kan yakin basasar Najeriya, wanda ‘yan Najeriya da dama suka bayyana a matsayin abin kyama.

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, mai matukar goyon bayan wannan gwamnati, shi ma ya wallafa a shafinsa na Twitter ranar Lahadi duk da haramcin.

A yayin korafin jama’a da suka da suka biyo bayan shawarar da gwamnatin ta yanke, Malami a ranar Asabar din da ta gabata ya umarci Daraktan Lauyoyin da ke gabatar da kara a ofishinsa da ya fara aikin gurfanar da wadanda suka karya dokar dakatar.

A wani sako da ya gabatar a shafinsa na Facebook da aka tabbatar a ranar Talata, Babban Lauyan ya wallafa wani hoto daga shafin Twitter wanda ke nuna an goge shafin nasa

“Shafi na, na Twitter na goge shi” in ji shi.

Amma hakan ya nuna cewa ba za a iya goge shafin Twitter ba sai dai idan mutum yayi amfani da manhajar, ma’ana Malami dole ne ya shiga don goge shafinsa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *