Wani mutum mai kimanin shekaru 20 ya yanke kan kakarsa, ya kuma sanya kan a cikin bakar leda, sannan ya kai shi ofishin ’yan sanda na Kisumu da ke Kenya.
Mutumin ya girgiza jami’an ‘yan sanda lokacin da ya isa ofishin da bakar ledar, kuma ya nemi jami’an su bude ledar a ranar 5 ga Afrilu.
A lokacin da suka bude ledar, sai suka sami sabon yankakken kan mutum.
A wani bidiyo mai dauke da hoto da aka yada a shafin Twitter, an ga ‘yan sanda a cikin mota, inda suka raka wanda ake zargin zuwa inda aka aikata laifin a Nyalenda Estate don gudanar da bincike kan kisan.
A cewar gidan talabijin na TV47 Kenya, nan da nan aka kwashe gawar kakar daga wurin.
Har yanzu ba a bayyana dalilin da yasa mutumin ya aikata wannan laifin ba, ko da yake jami’an tsaro na akan bincike.