fbpx
Wednesday, May 12
Shadow

Babbar mota ta murkushe mata 10 har lahira a kasuwar Jihar Imo

Wata babbar mota da ta kutsa cikin kasuwar Nkwommiri da ke karamar hukumar Nwangele ta jihar Imo a ranar Asabar 1 ga watan Mayu, rahotanni sun nuna cewa motar ta murkushe wasu mata 10 har lahira.

Wasu da dama kuma sun jikkata sakamakon motar da ta rasa birki yayin sauka daga hanyar Anara zuwa Orlu.

Matan da ke kasuwanci a bakin hanya, an murƙushe su a cikin wani kogi da ke kusa.

Wani ganau ya shaida wa manema labarai cewa al’ummar suna aiki tare da jami’an gwamnati don ceto wadanda suka makale.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *