fbpx
Wednesday, June 23
Shadow

Babbar mota ta murkushe yan talla biyu har lahira a kan babbar hanyar Legas zuwa Ibadan

Wani mummunan lamari ya faru a kusa da Lotto, inbound Lagos akan babbar hanyar Legas zuwa Ibadan a ranar Juma’a 4 ga watan Yuni yayin da wata babbar mota ta murkushe wasu mutane 2 har lahira.

Lamarin ya faru ne da misalin karfe 3:30 na yamma kamar yadda Mista Babatunde Akinbiyi, kakakin hukumar kula da bin doka da oda (TRACE) ya tabbatar.

An gano cewa direban babbar motar mai lambar SMK 82 XY, ya rasa yadda zai yi, sai ya kauce daga kan hanyar ya afka wa wasu mata biyu masu talla akan hanyar, kuma nan take suka mutu.

An ajiye gawarwakin a dakin ajiye gawarwaki na Idera da ke Sagamu, yayin da wasu mutane uku da suka jikkata an kai su asibitin Famobis, Mowe.

A halin yanzu, an kai motar zuwa ofishin ‘yan sanda na Mowe, tare da direban domin gudunar da wani bincike.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *