fbpx
Thursday, August 5
Shadow

Babu mafi kyaun matashin da zai shugabanci Najeriya kamar Yahaya Bello – Mikel Obi

Tsohon kyaftin din Super Eagles, Mikel Obi ya ce babu wani matashi da ya fi dacewa da ya gaji Shugaba Muhammadu Buhari kamar Gwamna Yahaya Bello na Jihar Kogi.

Mikel, ya yi wannan tsokaci ne yayin wata ziyarar ban girma da suka kaiwa gwamnan.

Tsohon dan wasan na Chelsea ya ce Najeriya ta isa lokaci don samar da shugabanci na matasa.

Mikel ya kuma yi alƙawarin tallafa wa burin Bello na siyasa gabanin 2023.

Ya ce ya kamata a ba matasa dama su samu canjin da ake nema.

“Wane mutum ne ya fi dacewa ya jagoranci matasa fiye da shi, saboda yana yin duk waɗannan kyawawan ayyukan kuma shi ya sa nake nan don ganin duk hanyar da zan shigo.”

Don hada kan matasa su sani kuma su ga yadda za mu inganta abubuwa ga kasarmu da kuma yadda za mu hada kai don cimma duk wannan, ”inji shi.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *