fbpx
Monday, October 25
Shadow

Babu maganar tsarin karba-karba a kundin tsarin mulki>>Gwamnonin Arewa suka gayawa na kudu

Gwamnonin kudu a wani taro da suka yi a watan Yuli sun nemi cewa, mulkin Najeriya ya koma yankin nasu a shekarar 2023.

 

Saidai a taron da suka yi, gwamnonin Arewa 19 sun mayarwa dana kudun martanin cewa mulki ba na karba-karba banr kamar yanda kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanadar.

 

Gwamnonin sun ce ba za’a tursasa Arewa kada ta nemi shugaban kasa a shekarar 2023 ba dan kuwa kundin tsarin mulki ya bata damar yin hakan.

 

Sun ce duk da yake ana iya baiwa kudu damar yin mulki a shekarar 2023. Amma dai a zahiri gaskiya ba abune na dole-dole ba.

 

Gwamnan jihar Filato, Simon Lalong ne ya bayyana haka a sanarwar bayan taron da ya fitar.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *