fbpx
Wednesday, October 20
Shadow

Babu ranar bude layukan sadarwa a Zamfara>>Gwamna Matawalle

Gwamnan Zamfara Bello Muhammad, Matawallen Maradun, ya ce babu ranar buɗe layukan sadarwa a jiharsa.

A ranar juma’a wa’adin da gwamnan ya ɗiba na buɗe layukan ya cika, kuma a hirarsa da BBC ya ce babu ranar dawo da layukan sadarwar a jihar.

“Dole mu tsawaita don burinmu tabbatar da tsaron al’ummarmu,” in ji gwamna Matawalle.

Ya ce gwamnati za ta ci gaba da tattaunawa da jami’an tsaro, kuma makomar tattaunawar ce za ta tantance lokacin da za a buɗe layukan, ko za su ci gaba da kasancewa a rufe.

Fiye da mako biyu kenan da al’ummar Zamfara ke rayuwa babu hanyoyin sadarwa a faɗin jihar, matakin da hukumomi suka ce sun ɗauka domin ƙoƙarin magance matsalolin ƴan bindiga masu kai hare-hare da satar mutane a jihar.

Matakin toshe layukan na sadarwa ya shafi yankunan jihar Katsina da ke makwabtaka da jihar Zamfara.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *