fbpx
Friday, April 23
Shadow

Babu Wanda ya isa ya kifar da Gwamnatin Shugaba Buhari>>Garba Shehu

Babban mataimaki na musamman akan kafafen yada labarai ga shugaban kasa Muhammadu Buhari, Malam Garba Shehu yace, babu wanda ya isa ya rusa gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari.

 

Da yake mayar da martani ga masu fafutuka a kasa nan irinsu Sunday Igboho da Asari Dakubo, Shehu ya ce da dama daga cikin wadannan mutanen ana daukar nauyinsu ne domin su rika muzanta gwamnatin Buhari, suna tunanin kamar za su iya tilastawa gwamnatin ta mika wuya.

 

Igboho dai ya na cewa, mafi yawan albarkatun kasar nan suna hannun mutanen arewa, kuma ana ta kashe yarabawa a kasarsu babu wanda ya damu.

 

Dakubo kuwa cewa ya yi ya kafa gwamnatin al’umar Igbo Biafra wadda za ta samu hadin kan wani bangare na yankin Kudu maso Gabas da Kudu maso Kudu su zama mallakarsu.

 

Garba Shehu ya yi wannan martani ne a gidan talabijin na Channels, inda ya kara da cewa babu wanda ya isa ya kori gwamnatin shugaba Buhari ta hanyar shafa mata bakin fyanti.

 

A baya dai, Hutudole.com ya kawo muku Rahoton yanda shugaba Buhari ya gayawa wakilam kasashen waje cewa, Najeriya na da kamanceceniyar zaman lafiya dasu

 

“I want to assure Nigerians that the administration of President Muhammadu Buhari is addressing multiple challenges that are facing the country especially in dealing with security and yet we are still making progress in agriculture, economy, anti-corruption, which are the key policies that brought the party and the government to office.

 

“It is sad for the country that opposition is exploiting some of these things. It is quite unfortunate and I want to assure that the president remains focused in preserving the security and unity of this country.

 

“It is an established fact that all nations of the world face problems and what is expected of all well-meaning members of the society is that they should team up with the government so that together we will all fight criminality and insurgency and all that.

 

“We accept that dissent is allowed, this is a democracy and people have a right to tell truth to government but we must be careful in doing that. Nobody can bring down the government because this is a government elected democratically.

 

“Government in a democracy come through periodic elections and if we have a government in office as we have, sponsored by political parties to win the elections, it is telling you that that confidence of the public is still there.”

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *