fbpx
Monday, September 27
Shadow

Babu wanda ya tsira a Najeriya>>Sule Lamido

Tsohon gwamnan jihar Jigawa kuma jigo a jam’iyyar adawa ta PDP Sule Lamido ya bayyana damuwarsa kan halin tsaron da Najeriya ke ciki, yana cewa “jini ne ke zuba a ko ina a kasar.

Yayin wata ziyara da ya kai wa tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo, a Abeokuta ya ce har yanzu Najeriya na zuciyar shugaban duk da kalubalen da take fuskanta.

Cikin wata sanarwa da mataimakin Obasanjo kan harkokin yada labarai Kehinde Akinyemi, ya fitar ya ce Lamido ya ga Obasanjo cikin koshin lafiya.

Quote Message: Yadda za ka kasance cikin aminci shi ne babban kalubalen Najeriya, saboda yanzu babu wanda ya tsira, dubi yadda masu garkuwa da mutane suka sace ma’aikatan Baba tsohon shugaban kasa? to wanene ya yi saura? in ji Sule Lamido.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *