fbpx
Monday, November 29
Shadow

Babu wani shirin bayar da tallafin Dubu biyar-biyar, maganar fatar bakice kawai, Majalisa ta tonawa Gwamnatin tarayya Asiri

Majalisar Dattijai tace babu shirin biyan Naira Dubu biyar-biyar da gwamnatin tarayya tace zata maye shi da tallafin man fetur a kasafin kudin shekarar 2022.

 

Shugaban kwamitin majalisar dake kula da bangaren kudi, Sanata Solomon Adeola Olamilekan ne ya bayyana haka.

 

Yace akwai dai tanadin biyan tallafin man fetur a cikin kasafin kudin amma babu maganar biyan Naira Dubu biyar-biyar.

 

Hakan ya sabawa maganar da Ministar kudi, Zainab Shamsuna Ahmad ta yi na cewa sun tanadi baiwa ‘yan Najeriya tallafin Naira Dubu biyar-biyar duk wata dan rage musu radadin cire tallafin man fetur din.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *