fbpx
Thursday, September 23
Shadow

Bacci ya dauke wani barawon wayoyi a Jihar Kebbi, yayin da yake sata cikin masallaci

Wani mutum ya cafke wani barawo mai suna Hamza Usman a lokacin Sallah Subhi yayin da yake bacci a cikin masallaci.

 

An bayyana cewa an kama Usman, wanda ya fito daga ƙauyen Maidahini, da sanyin safiyar ranar 30 ga Yuli, tare da wayoyin hannu da yawa a Bayan Kara, Birnin Kebbi, babban birnin jihar Kebbi.

 

Wani bawan Allah mai suna Yakubu Ahmed BK yace; Wanda ake zargin ya kutsa cikin wani masallaci a jihar Kebbi don yin sata kuma an damke shi bayan ya gaji ya yi barci.

 

Wanda ake zargin da satar wayoyin ya yi ikirarin cewa yana tare da wasu mutane biyu wadanda a halin yanzu sun tsere inda ya kara da cewa sun dade suna satar wayoyi a cikin gidaje lokacin da mutane a lokutan da suke bacci.

 

An tattaro cewa Usman ya shiga masallacin da daddare bayan ya ketara gidajen mutane tare da satar wayoyi kuma yana shirin satar wasu abubuwa a cikin masallaci sai kwatsam bacci ya dauke shi.

 

An kama Usman lokacin da wani mutum wanda ya fara shiga cikin masallaci domin samun jam’in sallar asuba.

 

An kuma kara da cewa tuni aka mika Usman ga ‘yan sanda domin ci gaba da yi masa tambayoyi.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *