fbpx
Friday, April 23
Shadow

Badaru, Bagudu, Barkiya Sun Bada Gudummawar Naira Miliyan 60 Ga Wadanda Gobara Ta Shafa a Kasuwar Katsina

A ranar Laraba ne gwamnan jihar Jigawa, Muhammad Badaru Abubakar, da takwaransa na jihar Kebbi, Abubakar Atiku Bagudu, suka ziyarci Gwamna Aminu Masari don yi masa ta’aziyya tare da sauran al’ummar jihar Katsina kan gobarar da ta lakume wasu sassan babbar kasuwar ta Katsina.
Gwamnonin biyu sun sanar da bayar da gudummawar naira miliyan 20 kowannensu a matsayin gudummawar da suka bayarwa don dakile illar gobarar tare da taimaka wa wadanda abin ya shafa.
Sun roki Allah Madaukakin Sarki da ya sake cika duk abin da ya ɓace yayin tashin wutar kuma ya kiyaye afkuwar hakan a nan gaba.
Hakanan, Sanatan da ke wakiltar shiyyar Katsina ta Tsakiya, Kabir Abdullahi Barkiya, ya ba da gudummawar miliyan N20 ga wadanda bala’in gobara ya shafa a kasuwar ta Tsakiya.
Barkiya ya bayar da gudummawar ne a jiya Laraba lokacin da ya ziyarci kasuwar da abin ya shafa domin jajantawa ‘yan kasuwar kan bala’in.
Sanatan ya bukaci wadanda lamarin ya rutsa da su da su dauki abin da ya faru a matsayin kaddara, ya kara da cewa babu adadin kudin da zai biya diyyar asarar da suka yi, yayin da ya yi addu’ar Allah ya kawo masu dauki ya biya su.
A jawabinsa, Gwamna Masari ya nuna matukar jin dadinsa ga duk wadanda suka nuna damuwa kan lamarin, yana mai cewa tuni mutane suka fara ba da gudummawar kudi ko da ba tare da kafa wani asusun neman tallafi ba don taimaka wa ‘yan kasuwar da abin ya shafa.
Masari ya ce ya zuwa ranar Talata, sama da gudummawar miliyan N170 aka samu daga masu bayar da tallafi daban-daban.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *